Wasu fusatattun matasa da ba a san ko suwaye ba, sun yi lakadawa fitacciyar matashiya ‘yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya dukan tsiya a yammacin alhamis a Kano.
Alfijir Labarai ta rawaito hotunan Murja sun bayyana a shafukan sada zumunta wanda aka canza mata kamanni da raunuka a fuskarta.
Tuni dai aka fara yin kira ga jami’an tsaro da su bi mata hakkinta ta hanyar zakulo wadanda suka yi mata wannan aika-aika.
Murja Ibrahim Kunya dai tayi kaurin suna a shafin TikTok inda take da mabiya masu dimbin yawa,dake bibiyar shafin nata.
Kuma yar gwagwarmayar siyasa ce da take goyon bayan Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb