Wasu ƴan bindiga sun kai hari tare da ƙone gidan ɗan majalisa Kurmus

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kona gidan Canice-Moore Nwachukwu, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Orlu/Orsu/Oru ta gabas ta jihar Imo.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa jaridar TheCable cewa lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis.

A cewar majiyar, maharan sun kai farmaki gidan da ke Isioma a kauyen Abara na unguwar Amanator Okporo a karamar hukumar Orlu “da bindigogi, bama-bamai, da sauran muggan makamai”.

Ya kara da cewa maharan sun yi garkuwa da ma’aikatan cikin gidan, kuma sun “yi bidiyo na ma’aikatan” kafin su yi awon gaba da wasu kayayyaki da kadarori masu daraja tare da kona gidan.

Maharan sun zuba fetur, wanda suka shigo da shi gidan, bayan sun wawwatsa a ko ina na gidan suka banka wuta.

Bayan kammala wannan Ta’addancin ne, sai su fita da ganimar da suka diba.

” Henry Okoye, kakakin rundunar ‘yan sandan Imo, ya tabbatarwa da faruwar lamarin.

Okoye ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin tare da cafke wadanda suka aikata laifin cikin gaggawa.

A ranar 8 ga watan Agusta, wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kona gidan Jerry Alagbaoso, tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar Orlu/Orsu/Oru gabas.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *