Kasha Sauki Communications Center yayin bikin Murnar Zagayowar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Sallahu Alaihi Wasallim, tsira da aminci su kara tabbata a gare shi, wanda kamfanin ya saba gabatarwa duk shekara a babban ofishin sa dake garin Kano a unguwar Yola, ya karrama jaridar Alfijir Labarai da lambar yabo.

Da yake karin haske kan lamarin shugaban kamfanin Alh Usman Khamis (Kasha Sauki) ya bayyana dalilan ya yasa suka karrama Alfijir Labarai da sauran wasu abokanan hurdarsu a wannan wata na Maulidi.
Ya kara da cewar sun fito wannan karramawar ne a wannan shekara sakamakon baya da Maulidin kawai suke yi.
Kasha Sauki yace yana da kyau a matsayinka na musulmi ka nuna murna da farin cikin ka na wannan wata, ko da ba za zaka hada taro ba yana da kyau kayi wani abu na musamman domin Annabi, duba da muma da muna hada murnar zagayowar kasarmu shekara da wasu manyan kasarmu da kuma mu kanmu.

A nasa bangaren babban manajan kamfanin Bashir Yusuf Bala (Alhajin Kasha Sauki) ya ja hankalin al’umma kan yin gaskiya da rikon amana, wanda shine ya kaini ga wannan matsayi, tun dag yaron kamfani na karshe yanzu na zama nine na biyu a kamfanin.
Yanzu haka kamfanin yana da reshina daban daban, wanda har koyar da gayaran yara yake yi.
Kasha Sauki Communications Center ya shahara ne wajen siyaar da dukkannin kayan wayar kowace irin da ita kanta wayar, sannan kuma suna yin gyaran wayar da koyar da gyaranta gaba daya.
Kasha Sauki Communications Center yana da rassa kamar haka:-
No. 3 Yola Madaki street kano.
No. 63 Dan suleka farm center kano.
No 120 Yamadawa junction kano.
No 74 from center kano layin ‘yan jagwal.
Manajan ya kuma ya hankalin alumma wajen nuna farin cikinsu ga wannan rana domin hadisi ya tabbatar da babban Annabi S A W, murna da yayi da kuma yanta baiwa saboda haihuwar Shugaba S A W, Allah baya yi masa azaba duk litinin.


Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb