Mutanen waɗanda ke karatu a kwalejin Ilimi ta Zuba da Abuja, sun musulunta ne , biyo bayan jawabin karɓar Ƙaddara Da Su Ka Ji Maryam Shetty tayi a lokacin da aka cire Sunanta daga ministocin Tinubu.
Alfijir Labarai ta rawaito Sama da mata 50 sun musulunta a kwalejin ilimi ta Zuba da ke birnin tarayya Abuja sanadiyyar sarauniyar Matasan Arewa, Dakta Maryam Shetty.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da Shettin ta fitar a shafinta cikin wani saƙon cewar ita musuluntar da mutanen da aka turo mata daga makarantar.
A cikin saƙon an bayyana cewa rungumar ƙaddara da Maryam ta yi lokacin da aka cire sunanta daga cikin jerin ministocin Nageriya a gwamnatin Tinubu shi ne ya yi silar musuluntarsu.
Kamar yadda su ka ce: “Hajiya Maryam mu na sanar da ke cewa muna da waɗanda ba musulmai ba sun karɓi musulunci, ko da a yau ma, an samu ƙarin wata mace ta musulunta.
Hakan ya faru ne dalilin Imani da kika nuna na karɓan ƙaddara, lokacin da aka cire sunanki a matsayin minista.
Ranki ya daɗe idan har kin ba da dama zan gabatar da su a gare ki”. Kamar yadda yake cikin saƙon.
Saƙon ya cigaba da cewa: “Tuni mun sanya su a makarantar Islamiyya ta (Nusret Educational and cultural limited) da ke Jabi, Abuja.
Mun ɗauki nauyin karatunsu da abincinsu, wasu daga cikinsu suna matuƙar buƙatar ki tallafe su da gudunmawa kamar: Qur’ani, Dardumar Sallah, Jallabiya da Carbi, da sauransu.
Mun gode.
A nata ɓangaren, Maryam Shetty ta bayyana jin daɗinta gami da godiya ga Allah bisa faruwar wannan al’amari na musuluntar mutane a sanadiyyarta.
“Alhamdulillah, wannan daga Allah ne”. In Ji Shetty
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb