Murnar Mauludi: Ƙungiyar Muryar Darika Ta tallafawa Mata 141 Da Jarin Sana’a

Daga Shu’aibu ibrahim Gusau

Sakamakon Zagayowar watan maulidi, wata kungiyar Muryar Darikar Tijjaniya ta koyawa Mata 141 sana’ar yi tare da basu tallafin Jarin Naira dubu biyar ga kowace mace .

Alfijir Labarai ta rawaito da yake gabatar da jawabin sa, shugaban gidauniyar tallafin ta Muryar Darika, Malam Nuhu Kabir ya bayyana cewa,su mambobin kungiyar ne ke samar da wannan tallafin a tsakanin duk juma’ar karshe wata , wanda muke gabatar da zikirori, a nan ake samar da wannan kudadan tallafin, tare kuma da tallafin wasu daga cikin mu wanda a nan ne wasu su ke bada tallafi me tsoka domin tallafawa marasa karfi.

Ya ce a wannan karon tallafin naira dubu dari bakwai da haminsinne zasu bada wanda mata 141 zasu amfana da shi, musamman masu kananan sana’oi Kamar sana’ar Kuli kuli da Cincin da zobo da Kosai da kuma Awara da Madarar Waken Soya.

A nasa jawabin Shugaban Majalisar Shura ta kungiyar liman Abduraham Jibil ya bayyana cewa, Muryar Darika ta kashe sama da naira miliyan 8 wajan tafiyar da ayyukan ta da tallafawa marasa karfi da masu kanan sana’a cikin wannan Karamar Hukumar ta Funtua.

Shima Khalifa Ali Saidu Alti ya bayyana cewa, saboda murnar haihuwar Manzon Allah (S A W) a wannan watan ne ya sa muka ba da tallafin albarkacin Manzon Allah (S A W) kuma wannan umarni ne na Manzon Allah (S A W).

Babban bako shine gwamnan Jihar katsina Umar Rada wanda ya samu wakilcin Abdulraham Nasir Funtuwa, gwamnan ya bayyana jin dadinsa akan kokarin da Muryar Darika keyi na tallafawa masu kanan karfi da jarin sana’a, Kuma ya ce wannan yayi daidai da kudirin gwamnatin Jihar katsina, wanda ya ce gwamnati zata samar da hukuma a karkashin ofishin sa dan taimaka wa masu karamin karfi bangaren sana’oinsu .

Akan haka ne gwamna Rada yayi kira da kungiyoyi da suyi koyi da Muryar Darika Tijjaniya Funtua, wajan bada tallafin sana’a, da kuma yiwa kungiyar rijista ta jiha da gwamnatin tarayya dan cin moriyar gwamnati.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *