An garzaya da wanda aka yi garkuwa da shi da wanda aka jikkata zuwa babban asibitin Babura domin yi musu magani
Alfijir Labarai ta rawaito ranar lahadi din data gabata bayanai daga majiya mai tushe ta nuna cewa, wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka kai farmaki Kwanar Garki a karamar hukumar Babura,

Kakakin Rundunar yansandan Jihar Jigawa DSP Lawan Shiisu Adamu ya bayyana yadda masu garkuwa suka yi garkuwa da wani Isyaku Umar mai shekaru 37 a Kofar Arewa Babura LGA suka kuma harbin wani Ahmad Abdullahi mai shekaru 30 da haihuwa a kauyen Babbar Ruga a hannunsa.
Bayan samun rahoton, tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO na Shiyya ta Babura, suka garzaya wurin da lamarin ya faru tare da ceto wanda aka yi garkuwa da shi cikin aminci.
An garzaya da wanda aka yi garkuwa da shi da wanda aka jikkata zuwa babban asibitin Babura domin yi musu magani.
An yi wa wanda aka yi garkuwa da shi magani sannan aka sallame shi, ya kuma sake haduwa da iyalansa.
A halin yanzu, Ahmad Abdullahi wanda masu garkuwa da mutane suka harba, an kai shi asibitin koyarwa na Rashid Shekoni dake Dutse.
A ci gaba da kiran da aka samu daga sashin Babura na cewa, masu garkuwa da mutane sun nufi yankin Ringim.
Jami’in ‘yan sanda na yankin Ringim, tare da tawagar ‘yan sanda da ‘yan banga, sun tsaya da bincike a kauyen Daushe da ke kan titin Ringim Kanya Babba.
Da ganin ‘yan sandan, ‘yan fashin sun bar motar su ta Vectra suka ranta a na kare.
Yayin bincike ansamu mota kirar Vectra, mai lambar NEN 20 NZ ANAMBRA STATE, bindiga AK 47 daya (1), mujalla daya (1), harsashi guda goma sha biyar (15) da kuma wayar Android.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, CP Effiom Emmanuel Ekot ya yaba da kokarin ‘yan sandan na aikin weldon, ya kuma umarce su da su tsaya tsayin daka domin ganin an kama masu laifin da suka gudu tare da hukuntasu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb