Hedikwatar tsaro, DHQ, ta ce dakarun sojin Najeriya, a cikin makonni biyun da suka gabata sun hallaka jimillar ƴan ta’adda 151 tare da kama wasu 456 a wasu hare-hare daban-daban a fadin kasar.
Alfijir Labarai ta rawaito Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo-Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan yayin da ya ke bayar da karin haske game da ayyukan sojoji a fadin kasar a yau Alhamis a Abuja.

Buba ya ce dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda 44, sun kuma kama 21 tare da kubutar da wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su a lokacin.
Ya ce sojojin sun kwato bindigogi kirar AK47 guda 17, bindigu korar gida guda uku, bindiga kirar berretta daya, bindigogin Danish guda uku da kuma alburusai 116 na musamman masu girman 7.62mm.
Har ila yau, a cewarsa, an ƙwato harsasai masu girman 7.62mm na NATO, masu girman 9mm 13, 7.62 mm x 54 ammo guda 20, 42.
Sauran sun hada da gidan jera harsashi 12, jarkoki 50 na fetur motoci uku, wayar salula biyar, babura shida, adduna uku da kuma kudi naira miliyan 3.18.
Mista Buba ya ce sojojin sun kama wasu da ake zargin suna da alaka da ‘yan ta’adda a Jere da Biu a Borno, da kuma karamar hukumar Gujba a Yobe.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb