Shugaban kungiyar APC Intellectual Forum A.K. Mustapha ya ja hankalin Gwamna Abba Kabir a kan cika alkawarin da ya dauka a kan ilimi.
Alfijir Labarai ta rawaito kungiyar APC Intellectual Forum (AIF) ta yaba da kokari da alkawuran da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi na biyan kudin Makaranta da ya kai 11,827,000 na Ɗalibai mata 100 a Jami’ar Bayero.
Sanarwar ta kara da cewa wannan karimcin ya dace a yi koyi da shi, musamman gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya yi alkawarin biyawa daukacin Ɗaliban jihar kudin makaranta ba iya na Jami’ar Bayero, amma gwamnatinsa ta kasa cika alkawari.
Da yake jinjina irin karramawar da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi na biyan kudin, ya kuma yi
roko ga Gwamna Abba ya cika alkawarin da ya dauka, kasancewar Jami’ar Bayero za ta rufe biyan kudin rijistar dalibai a yau.
Kungiyar APC Intellectual Forum, tana rokon Allah Madaukakin Sarki da ya sakawa Gawuna da Kyakkyawan alheri amin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb
To kafun gawunan yabiya waya fara biya? Kuma abunda gwamnan mu yayi kafun ynx ku kuka gaya mai yanda zaiyi?