Lamarin ya afku ne a Mazaɓan Sale Mai Agogo dake Rijau Central Ward a jihar Neja.
Alfijir Labarai ta rawaito lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe uku da wasu mintuna inda jami’an tsaro suka yi harbi, nan take harsashin ya samu wani yaro da kuma wata mata tsohuwa.
Yanzu haka da yaron da matan an garzaya da su asibiti, ɗaya na asibitin Kauna dake ƙaramar hukuman Rijau, ɗaya kuma na asibitin Hamdala.
Lokacin da abin ya faru likitocin waɗannan asibitocin basu taɓa ko ɗaya daga cikinsu ba, illa ruwa kawai da suka ɗaura masu, kasancewar babu wani shugaba ko jagora da ya halarci wannan asibitin.
Kamar yadda likitan asibitin Hamdala yace, shi ba zai iya yima wannan yaro aiki ba, sai dai ya ɗaura masa ruwa, daga nan a ɗaukeshi a kai shi babban asibiti.
Muna kira zuwa ga manyan Rijau da su kaiwa waɗannan mutane agaji, tare da tallafa masu, da kuma yin sahihin bincike akan wanda yayi harbin da kuma dalilin da yasa yayi harbin, saboda mutanen suna ɗaya daga cikin ƴan gudun hijira, ance mutanen ƙauyen Inana ne.
Rariya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb