Wasu tagwayen hare-haren ta’addanci a kasar Mali sun halaka fafaren hula 49 da sojoji 15

Wani soja da ya bukaci kamfanin dillancin labarai na AFP ya boye sunansa ya ce an kai wa jirgin ruwan hari ne da rokoki, kuma sojoji na ci gaba da aikin ceto.

Rahotanni daga kasar Mali na cewa, an kai wasu hare-haren ta’addanci guda biyu a kasar, inda aka auna wani jirgin ruwan fasinja da kuma wani sansanin soji dake arewacin kasar.

Lamarin da ya haddasa kisan mutane 64, da suka hada da fararen hula 49 da sojoji 15. Mahukuntan kasar Mali sun sanar da zaman makoki na kwanaki uku tun daga Jumma’ar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, wata kungiya mai alaka da al-Qa’ida ta yi ikirarin kai wadannan hare-hare.

Wani soja da ya bukaci kamfanin dillancin labarai na AFP ya boye sunansa ya ce an kai wa jirgin ruwan hari ne da rokoki, kuma sojoji na ci gaba da aikin ceto.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *