Uwar gidan tsohon shugaban kasan ta bayyana damuwa kan lamarin ne a shafinta na Facebook jiya Lahadi, inda ta yi kakkausar suka ga wata mata tana mai cewa likitocin Najeriya da tsarin kiwon lafiya suna salwantar da rayuka.
Alfijir Labarai ta rawaito mai dakin tsohon shugaban kasa Buhari na cewa, a kasa da watanni uku bayan mijinta, ya bar mulki harkar lafiya ta kara tabarbarewa, biyo bayan wani faifan bidiyo na wata mata tana zagin asibitoci da likitocin Najeriya saboda salwantar da rayuka da yake yawo a yanar gizo.
Aisha ta kara bayyana sukar wata mata sanye da gilashi da hijabi ruwan Madara tana mai cewa likitocin Najeriya da tsarin kiwon lafiya suna “sakaci ga rayuka.”
A Najeriya ta faru da ni, An lalata rayuwar ɗana da kuskure daga likita,” matar ta fada ta na yin kuka.
“Wannan yana daya daga cikin dubban yara da ke can da kuma iyalai da tsarin ya illata.
“Lokaci ya yi da za mu fara amfani da tsarin (sic) na bayyana sunayen asibitocin da ke illata al’umma,
Za mu kama ku da alhakin ayyukanku.
Ta yaya babban asibitin gwamnati, ba shi da injin daukar hoto,” inji matar.
Mu dai a nan ba za mu iya tabbatar da ikirarin matar na cewa wani likita dan Najeriya ya lalata rayuwar danta ba.
Duk da haka, matsayinta ya yi dai-dai da sukar Aisha Buhari a kan tsarin kiwon lafiyar Najeriya.
A shekarar 2017, a tsakiyar wa’adin mulkin mijinta na farko, Aisha Buhari ta yi tsokaci game da fannin kiwon lafiyar Najeriya, inda ta bayyana hakan a matsayin wanda ta gaza.
“Kafin in fara magana ta, zan so in fadi wasu kalmomi game da kiwon lafiya a Najeriya da tsarin samar da lafiya a Najeriya, abun ya zama mai matuƙar ban takaici, a yi hakuri da faɗin haka, ”in ji ta.
Shugaba Buhari ya yi wa’adi biyu na shekaru takwas tsakanin 29 ga Mayu, 2015 da 29 ga Mayu, 2023.
A tsawon mulkinsa, shugaban ya tafi London domin jinya, A cikin shekaru takwas da ya yi ya na mulki, ya kwashe sama da kwanaki 200 a wani asibiti a London ya na jinyar wasu cututtuka da ba a bayyana ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
AI MUDA SU BUHARI DA TAWAGAR GWAMNATIN SA SAI DAI ALLAH YA ISA
BAMU YAFE BA
ALLAH YBIMANA HAKKOKINMU