Yan biyun da suka kasance ‘yan takarar shugaban kasa a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
Alfijir Labarai ta rawaito tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso sun sake ganawa a Abuja a daidai lokacin da ake rade-radin cewa suna tattaunawa kan yiwuwar hadewar jam’iyyunsu domin kawo karshen mulkin jam’iyyar All Progressives Congress a Najeriya.
‘Yan biyun da suka kasance ‘yan takarar shugaban kasa a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fito a matsayin wanda ya lashe zaben, an ga ‘yan murmushi da hira a lokacin bikin Nikkah na Musa Jamilu Jibrin, dan Alhaji Jamilu Jibrin Lamido (Chokalin Adamawa) da Halima Abande Lawan. a Masallacin Annur.
Atiku ya bayyana hakan ne a dandalinshi na sada zumunta, inda ya ce, “A safiyar yau, na halarci bikin Nikkah na Musa Jamilu Jibrin, dan Alhaji Jamilu Jibrin Lamido (Chokalin Adamawa) da Halima Abande Lawan a masallacin Annur, Abuja.
Ina yi wa ma’auratan fatan alheri da albarkar aure.”
Ganawar tsakanin Atiku da Kwankwaso na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa sun yi ta tattaunawa kan yiwuwar hadewar jam’iyyun su PDP da kuma New Nigeria Peoples Party (NNPP).
Jam’iyyar APC mai mulki ta lallasa dukkanin jam’iyyun biyu a zaben 2023 mai zuwa.
Intelregion
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM