Hukumar DSS Ta Kama Shugaban Karamar Hukuma Kan Zargin Badaƙala

Shugaban karamar hukumar wanda ya zargi gwamnan da karkatar da kudade

Alfijir Labarai ta rawaito Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), reshen jihar Ogun, a ranar Juma’a, ta tsare shugaban karamar hukumar Ijebu ta gabas, Wale Adedayo, da aka dakatar, bisa zargin karkatar da kason kudaden kananan hukumomi.

Adedayo ya zargi gwamnan da rike kudaden kananan hukumomi a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ya kasance a ofishin DSS Abeokuta a ranar Juma’a, don amsa gayyatar da hukumar ta yi masa kan zargin.

Ya kuma kasance a ofishin DSS a ranar Alhamis kan wannan batu, amma an tsare shi a ranar Juma’a.

Daya daga cikin masu taimaka masa ya shaida wa Aminiya a daren Juma’a cewa mai yiwuwa Adedayo ya kwana a gidan yari a karshen mako.

Ya ce, “Tare muka zo nan na dauki wayarsa na tsaya a waje, tun a lokacin ba a bar shi ya fito ba.

“Bayan ya shiga wurin, shi ma gwamnan ya shigo ofishin DSS ya fita bayan mintuna 30.

Allah ne kadai ya san abin da ke faruwa da maigidana a yanzu, don Allah a taimake mu.

Karfe 8:34 na dare kuma har yanzu ba a bar shi ya fito ba.” In Ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *