A jiya Laraba ne jam’iyyar, APC, reshen jihar Osun, ta sanar da korar mambobinta 84, bisa aikata laifukan yi wa jam’iyyar zagon-ƙasa.
Alfijir Labarai ta rawaito wata sanarwa da shugaban jam’iyyar APC na jihar Osun, Sooko Lawal ya fitar, jam’iyyar ta dauki matakin ne biyo bayan korafe-korafen cin zarafin jam’iyyar da zagon-ƙasa da wadanda aka kora su ka yi.
“Bayan korafe-korafen da ake yi na yi wa jam’iyyar, sai kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC, reshen jihar Osun ya kafa kwamitin ladabtarwa da zai binciki zargin da ake yi wa wasu mambobin jam’iyyar.
“Wannan matakin ladabtarwar ya zo ne a matsayin mataki ga zarge-zargen da ake yi na rashin da’a da ayyukan da suke yinwa jam’iyyar zagon-ƙasa.
“Kwamitin ladabtarwa ya gudanar da nazari sosai ba tare da nuna son kai ba, kuma kwamitin zartarwas na jihar ya yi nazari sosai kan binciken.
“Bayan cikakken tantance shaidu da kuma yin la’akari da shawarwarin kwamitin, kwamitin zartarwas na Jiha ya dauki mataki mai wahala amma ya zama dole, shine na korar mambobin,” Inji shi.
Daily Nigerian
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM