Tinubu ya yi ala wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar Gabon, yana mai cewa, “mulkin kama karya” yana yaduwa a fadin nahiyar Afirka.
Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da sabon juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar Gabon
Shugaban ya nuna damuwarsa kan yadda juyin mulki ke yaɗuwa a Afirka, yana mai cewa ba zasu lamurci ci gaba da kwatar mulki da ƙarfin bindiga ba
Ya ce yana aiki tare da shugabannin ƙasahen ƙungiyar tarayyar Afrika domin ɗaukar mataki na gaba game da ƙasar Gabon
Tinubu ya yi ala wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar Gabon, yana mai cewa, “mulkin kama karya” yana yaduwa a fadin nahiyar Afirka.
Hakazalika Shugaba Tinubu ya bayyana matukar damuwarsa kan yanayin da ake ciki na dambarwar siyasa da zaman lafiya a kasar sakamakon hamɓarar da shugaban ƙasa.
Tinubu ya faɗi haka ne a martaninsa na farko kan juyin mulkin da aka yi a Gabon ranar Laraba, kamar yadda mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya bayyana.
A cikin sanarwar da kakakinsa, Mista Ngelale, ya fitar ya ce Shugaba Tinubu yana sa ido sosai kan halin da ake ciki a Gabon bayan kifar da zababɓiyar gwamnati.
Sanarwan ta ce: “Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na bibiyar abubuwan da ke wakala a ƙasar Gabon tare da nuna damuwa matuƙa kan halin da ƙasar ta tsinci kanta da kuma yaɗuwar mulkin kama karya a nahiyarmu da muke ƙauna Afirka.” “
“Tinubu, a matsayinsa na mutum wanda ya sadaukar da rayuwarsa, wajen kare Demokuraɗiyya, yana da yaƙinin cewa mulki ya zauna a hannun mutane na gari, ba a karɓe shi da bakin bingida ba.”
“Kan haka, shugaba Tinubu na aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran shugabannin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Afirka domin samun masalaha da ɗaukar mataki na gaba dangane da mulkin Gabon.”
Bugu da ƙari ya ce shugaban zai tattauna da sauran takwarorinsa da nufin cimma matsaya kan yadda zasu ɗauki mataki kan mulkin kama karyan da ke yaɗuwa a nahiyar Afirka.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
White lies, Greediness and Injustice of African Leadership are the cause of this Military intervention!
Shi Shi kam ina hankalinsa yake ne da jikinsa? Ai karin farashin mai da ya yi mana, ya fi juyin mulkin sojojin muni a garemu!
Kuyiwa Talakawa adalci kuzauna lafiya.
Da ya dawo da hankalinsa kan abinda ya addabi kasarsa na fatara da talauci da Hakan zaifi haifar masa da da Mai Ido.