Sojoji Sun Sanar Da Janar Nguema A Matsayin Shugaban Ƙasar Gabon

Jagororin sojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun sanar da Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban ƙasar na riƙon-ƙwarya.

Lamarin na faruwa ne ‘yan awanni bayan wasu sojoji daga rundunar tsaron fadar shugaban ƙasa sun zagaya da shi a titunan birnin Libreville don yin murna.

Ɗazu Shugaba Ali Bongo ya saki wani saƙon bidiyo daga gidan da ake tsare da shi, yana neman abokansa su ƙyamaci juyin mulkin – yayin da mutane ke ci gaba da murna a titunan ƙasar.

Shi da mahaifinsa sun mulki ƙasar da ke da arzikin man fetur tsawon shekara 56, amma da yawan ‘yan ƙasar na zaune cikin talauci.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *