Gwamnatin Katsina Ta Haramta Hawa Babur Da Dare A Kananan Hukumomi 19

Gwamnatin jihar Katsina ta haramta amfani da baburan hawa dana kasuwanci da dare a fadin kananan hukumomi 19 na jihar a wani mataki na inganta tsaro.

Alfijir Labarai ta rawaito wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Alhaji Nasiru Mu’azu, ya fitar, ya ce an dakatar da dokar ne daga karfe 8 na dare. zuwa 6 na safe.

Umarnin ya shafi Kananan Hukumomin da ‘Yan fashi da masu aikata sauran laifuffuka suka addaba.

Kananan Hukumomin sun hada da :-

Sabuwa.

Dandume.

Funtua.

Faskari.

Bakori.

Kankara.

Danja.

Kafur.

Malumfashi.

Musawa.

Matazu.

Danmusa.

Safana.

Dutsinma. 
Kurfi.

Charanchi.

Jibia.

Batsari.

Kankia.

Sanarwar ta kara da cewa ya kamata jama’a su fahimci cewa manufar wannan umarnin shi ne maido da zaman lafiya na dindindin a yankunan da abin ya shafa,” cewar sanarwar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *