Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya amince da rusa gine-gine 6,000 a gundumomi 30 na birnin.
Alfijir Labarai ta rawaito hukumar babban birnin tarayya Abuja tace, gine-ginen da abin ya shafa na daga cikin unguwanni 30 da aka gudanar da bincike a baya.
Idan dai za a iya tunawa Wike bayan rantsar da shi a ranar Litinin din da ta gabata ya sha alwashin dawo da babban tsarin na babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce za a ruguza duk wasu gine-ginen da ba su dace ba, kuma a shirye gwamnatinsa ta ke ta kawo karshen cece-kucen filaye.
Ya ce ya zagaya da daddare babban birnin tarayya Abuja domin ya ga al’amura da kansa, ya kuma koka da yadda tsarin mulkin yankin ya karkata da wasu gine-ginen da ba a saba gani ba a Abuja, yana mai cewa za a rusa su.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM