Musa Iliyasu Ya Maka Gwamnatin Kano Da Hukumar Karbar Korafe-korafe A Gaban Kotu

Tsohon kwamishinan ma’aikatar raya karkara Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya maka gwamnatin jihar kano da hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa a gaban kotu bisa karɓar wata mota da ya saya daga hannun sa.

Alfijir Labarai ta rawaito Musa ya garzaya babbar Kotun jihar kano mai lamba 4 wadda ke karkashin mai Shari’a Usman Na’abba Inda ya bukaci wadanda yayi kara da su biya shi kudin da ya kashewa motar wajen gyara da kuma kudin da ya sayi motar ko kuma a mayar masa da motar.

Barr. Badaru Sulaiman Ishaq shi ne lauyan Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso da yake zantawa da manema labarai yace tun da fari ofishin Sakataren gwamnatin jihar kano ne ya rubuta wanda yake karewa cewar ya mayar da wata mota kirar Hilux wacca aka yi masa gwanjon ta tun a gwamnatin data gabata.

” Ya Sayi wata mota ne ta gwamnati wacce ta lalace a hannun wani kamfani da gwamnatin ta yiwa gwanjon motar, sai kawai yaga takardar ana bukatar ya mayar da motar, shi ne ya sanar da mu cewa mu rubutawa gwamnatin yadda akai ya mallaki motar”. A cewar Barr. Badaru

” Mun rubutawa gwamnatin takarda cewar bashi da ja zai mayar da motar, Amma ga kudin da ya kashewa mota, don haka zai mayar da motar wajen bakanikensa don a cire masa abubuwan da aka sanyawa motar, ya mayar wa bakaniken motar a kofar ruwa kawai sai hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano ta turo aka dauke motar”. Inji Lauyan Musa Iliyasu Kwankwaso

Yace rashin basu amsa akan takarar da suka rubutawa gwamnatin ne yasa suka garzaya gaban kotu domin nemawa wanda suke karewa hakkinsa.

Barr. Badaru Sulaiman ya kuma ce a yayin zaman Kotun, lauyoyin wadanda ake kara basu kaiwa kotun bayanan kariya ba, amma suna da ragowar kwanaki kamar yadda dokar ta bayyana.

Tuni dai Mai Shari’a Na’abba ya dage zaman sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan October na shekara ta 2023 domin cigaba da Shari’ar.

Kadaura24

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *