Ina kira gare ku, ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa daban-daban ba, ku ba gwamnan jihar hadin kai domin ci gaban jihar Kano.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdulahi Ganduje, ya bukaci yan majalisar dokokin Kano da aka zaba a jam’iyyar APC da su yi aiki da gwamnan jihar, Abba Yusuf.
Ya ce, ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa ba, al’ummar Kano sun cancanci samun romon damakaradiyya, wanda dole ne su hada kai da gwamna domin cimma nasara.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin wasu yan majalisar dokokin jihar Kano su 14 da suka kai masa ziyarar ban girma a sakatariyar jam’iyyar a ranar Litinin a Abuja, ya ce dole ne su yi aiki domin ci gaban jihar Kano.
Da na ganku, ina tuna kaina ne domin wasunku suna tare dani shekaru 25 da suka gabata Wasunku sun ci zabe kuma sun kasance yan majalisa kuma sun fadi zabe sun dawo bayan shekara hudu. In Ji Ganduje.
Kun kasance a cikin aminci tare da ni, ban yi mamaki ba lokacin da na sami labarin kunzo nan don ganina a ziyarar taya murna ba.
Ganduje ya kuma yabawa ‘yan majalisar bisa gudunmawar da suke bayar wajen ci gaban siyasar jihar Kano.
Gwamnan jiharmu dan wata jam’iyya ce ta daban, amma ina so ku sani cewa gaba daya ma’anar siyasa ita ce ci gaban al’umma.
Ina kira gare ku, ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa daban-daban ba, ku ba gwamnan jihar hadin kai domin ci gaban jihar Kano.
Hakan ba zai hana ku ci gaba da rike matsayin ku na ‘yan majalisar jiha ba.
Bai hana mu hada kai don samun gwamnatin APC a jihar Kano ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne al’ummar Jihar Kano su samu ribar damakaradiyya.
Ina so ku yi aiki da gwamnati cikin lumana a jihar Kano kuma ina tabbatar muku da cewa za mu ba ku kwarin guiwa ta yadda za mu samu karin ‘yan majalisar jiha da ma har sai mun samu gwamna a jam’iyyarmu in ji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM