El-Rufai dai na cikin mutane 48 da shugaban kasa Bola Tinubu ya aika wa majalisar dattawa, sai dai har yanzu majalisar ba ta wanke shi ba saboda rahotannin tsaro da ake yi masa.
Alfijir Labarai ta rawaito Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya musanta labarin da aka yada a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa ya nuna adawa da nadin ministar da Nasir El-Rufai ya bayar na maye gurbinsa.
El-Rufai dai na cikin mutane 48 da shugaban kasa Bola Tinubu ya aika wa majalisar dattawa, sai dai har yanzu majalisar ba ta wanke shi ba saboda rahotannin tsaro da ake yi masa.
Bayan dakatar da nadin nasa, El-Rufai ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu a cikin mako guda inda ya shaida masa cewa ba shi da sha’awar zama minista, kuma ya ba da shawarar cewa tsohon kwamishinansa Jafaru Sani ya maye gurbinsa.
Sai dai Gwamna Sani ya musanta wani labari da ya taso a shafukan sada zumunta na cewa ya gana da shugaba Tinubu inda ya ki amincewa da Jafaru a kan cewa shi mai biyayya ga El-Rufai ne.
Gwamna Sani wanda ya bayyana labarin a matsayin zuki ta malle, a wata ganawa da gidan Talabijin na Channels cewa ya gana da shugaba Tinubu ne kawai domin tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka shafi nadin ministocin da ya gabace shi, kuma babu wani lokaci da ya sabawa ko kin amincewa da mutumin da El- Rufai ya bayyana.
Ya bayyana cewa wannan labarin na karya ne, kuma nufinsu haifar da rashin jituwa tsakaninsa da El-Rufai.
“Abin da ke gaskiya a labarin shi ne na gana da shugaban kasa.
Duk wani abu karya ne kuma hasashe ne don haifar da rikici tsakanina da Mallam (El-Rufai),” In ji shi.
“Na je ganin shugaban kasa musamman saboda na damu da yadda al’amura ke faruwa.
Na yi imani shi da El Rufa’i suna da amfani ga kasa.
“Babu wani lokaci da muka tattauna batun maye gurbinsa, wannan shine babbar damuwa ta kenan.
“Idan da gaske Mallam yana son ya zabi wanda zai maye gurbinsa, ba zan taba adawa da zabinsa ba.
Muna kan shafi daya, wadanda suka san mu sosai sun san cewa wannan duk karya ce.
Mun san daga ina aka samo asali amma ba mu damu ba.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM