A wani muhimmin mataki na kafa sabuwar gwamnati, Majalisar Dattawan Najeriya ta fara aikin tantance rukunin farko na Ministoci 28 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar.
Alfijir Labarai ta rawaito an gudanar da aikin tantancewar ne a zaman da aka yi a ranar Litinin, wanda ya fara da misalin karfe 12:41 na rana, bayan isowar shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
A yayin zaman, an tantance mutane 14 daga cikin wadanda aka nada, tare da hadakar gogaggun ‘yan siyasa da sabbin fuskoki a cikin wadanda aka tantance.
An tantance sunayen ministoci 14 Daga cikin fitattun wadanda aka nada akwai

Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas;
Abubakar Kyari daga jihar Borno;
Nkiruka Onyejeocha daga jihar Abia;
Bello Muhammad daga jihar Sokoto;
Sani Abubakar Danladi daga jihar Taraba;
Badaru Abubakar daga jihar Jigawa.
Joseph Utsev daga jihar Benue;
Olubunmi Tunji Ojo daga jihar Ondo;
Betta Edu daga jihar Cross River;
Uju Kennedy Ohaneye daga jihar Anambra;
Abubakar Momoh daga jihar Edo;
John Enoh daga jihar Cross River;
Iman Suleiman Ibrahim daga jihar Nasarawa;
Yusuf Maitama Tuggar daga jihar Bauchi.
Tsofaffin Sanatoci daga cikin wadanda aka nada an ba su kulawa ta musamman ganin irin gogewar da suka samu a majalisar.
Yayin tantancewar, Opeyemi Bamidele, ya gabatar da bukatar majalisar ta dawo zamanta tare da bayar da rahoto kan ci gaban da aka samu a lokacin tantancewar.
Wannan kudiri dai ya samu amincewar shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa,
Darlington Nwokocha, kuma majalisar ta amince da shi gaba daya.
Dangane da zaman, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya dage zaman majalisar har zuwa ranar Talata, inda ya ba da lokaci domin ci gaba da tattaunawa da kuma duba sauran ministocin da aka nada.
Yayin da Majalisar Dattawa ke ci gaba da tantancewa, ‘yan Najeriya na dakon jiran majalisar ministocin shugaba Tinubu, wadda ake sa ran za ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar kasar da kuma magance matsalolin da kasar da ake fuskanta.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb