Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama wata lauya mai suna Ebikpolade Helen, wacce ta kware wajen hadawa da rarraba skuchies, da cakuda wiwi, da wasu miyagun kwayoyi.

Alfijir Labarai ta rawaito wata sanarwa da kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ta ce matar tana zaune ne a unguwar Lekki da ke jihar Legas.
Mista Babafemi ya ce an kama wadda ake zargin ne a wani sumame da aka kai garin Awka a jihar Anambra, biyo bayan kama tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5 da kwalabe 12 da aka boye a bayan gidanta da ke Lekki.

Ya kuma ce an kama wani wanda ake zargin Abubakar Shuaibu a ranar 13 ga watan Yuli a Cappa, da ke titin Mushin-Oshodi dauke da kwalabe 86 na maganin tari na kodin.

Mista Babafemi ya ce magungunan da nauyinsu ya kai lita 8.6 suna cikin motar sa ta Toyota mai lamba FFA 241YB.
Kakakin ya ce an kama wasu mutane biyu Razak Ogunbo da Adeola Idowu a ranar 11 ga watan Yuli a Ikorodu dauke da lita 51 na skuchies.
An kuma gano tabar wiwi mai nauyin kilogiram 372 da kwalabe 48 masu nauyin lita 48 a gidan wani dillalin miyagun kwayoyi da ya gudu a Akala, ta Mushin da ke Legas a ranar 12 ga watan Yuli.
“A jihar Ondo, jami’an tsaro sun afkawa wani gini da ke Ehin-Ala, a karamar hukumar Akure ta Kudu, inda suka kama wani Abubakar Zayanu Gyambar mai shekaru 28, dauke da buhunan skunk guda 162 da nauyinsu ya kai kilogiram 1,944.

“An kama wani wanda ake zargi, Henry Wilson, mai shekaru 50, a garin Ogume, da ke Ndokwa ta Gabas, a jihar Delta, mai nauyin kilogiram 216.5,” inji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb