Mal Daurawa Ya Bayyana Yadda Za Su Gudanar Da Auren Zawarawa A Kano

Sabon Kwamandan Hisba na Kano  Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shiga ofis a karo na uku, bayan da gwamnan kano Abba Gida Gida sake nada shi a mukamin a ranar Litinin.

Alfijir Labarai ta rawaito yayin jawabin da ya gabatar a harabar hukumar kafin shiga ofis don fara aiki a ranar Laraba, ya yi godiya ga Ubangiji sannan ya neman hadin kan abokan aikinsa ‘yan Hisba da sauran ma’aikatan hukumar.

Cikin muhimman abubuwan da Daura ya ce zai mayar da hankali a kai a lokacin mulkin nasa, har da batun auren zawarawa.

Malam Daurawa ya bayyana cewar tuni gwamnan Kano Abba Gida-Gida ya bayar da umarnin a tantance mata da maza 2,000, wato mata dubu daya da maza dubu daya don a aurar da su bisa tallafin gwamnatin jiha.

Ya kara da cewa za a fara shirin auren ne da raba fom fom a kananan Hukumomin Kani 44. Kowacce karamar Hukuma za a ba ta fom guda 20.

Za a raba wa duk masu sha’awar auren don su cike tare da mika wa Hukumar.

Zai zama jumullar 880 kenan a kananan hukumomi 44, sai sauran 120 da za a rabar daga hedikwatar Hukumar da ke birnin Kano.

Bayan an dawo da fom da aka cike, sai kuma a zo a tantance a ga ko mutum ya cancanta ko bai cancanta ba don shiga shirin.

Hakazalika wadanda aka tantance aka tabbatar sun cika sharuddan da aka bayyana, sai a mika su ga hukumar ta Hisba. In Ji Daurawa

Bayan an tantance, za a shirya wa ma’auratan bita, za a ilimantar a su, a wayar musu da kai a kan mene ne aure, yaya ake zaman aure, mene ne hakkokin ma’aurata a kan juna da dai sauran su.

Bayan an shiryawa masu shirin angwancewa bita, Hukumar Hisba za ta hada kai da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano don tantance lafiyar wadanda za su yi auren.

Malam Daurawa ya ce, za a yi wa ma’auratan gwajin kwayar cutar HIV da ciwon sanyi da na nau’in jini da ciwon hanta da ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma na juna biyu.

Babbar manufar hakan ita ce don a tabbatar da lafiya da ingancin kowa, ta yadda wani ba zai cutar da wani ba.

Babban malamin ya jaddada cewar sai mutum mai cikakken hankali, wanda aka san asalinsa, mai sana’a da sanin ya kamata za a aurawa mace.

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa babban aikin Hisba shi ne Umarni da kyakkawan aiki da hani da mummuna, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya ba da umarni a ayoyi da dama na Kur’ani Mai Tsarki da kuma yadda Annabin Tsira ya yi umarni kuma aka gani a Hadisai.

Ya jaddada cewa dole ne a samu wani bangare na al’umma da zai dinga umarni da kyakkyawa da hani da mummuna kuma za a ci gaba da wannan aiki a dukkan fadin jihar Kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

One Reply to “Mal Daurawa Ya Bayyana Yadda Za Su Gudanar Da Auren Zawarawa A Kano”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *