Farashin man fetur ya karye a defo defo na Najeriya a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin ƙarin farashin man zuwa naira 700 a kan duk lita ɗaya cikin wannan wata na Yuli.
Alfijir Labarai ta rawaito ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya, IPMAN ta tabbatar da karyewar farashin, ta ce ana sayar da shi a kan naira ɗari huɗu da ɗoriya, saɓanin sama da naira ɗari biyar a kan duk lita ɗaya.
Danmalam ya shaida wa manema labarai cewa farashin ya karye ne saboda ƙarancin masu saye, kuma za a samu rangwamen har a gidajen mai.
Danmalam ya ce tun kafin tafiya hutun sallah, farashin man fetur ɗin ya fara sakkowa.
“A yanzu haka, man fetur a defo-defo ɗin da ke Lagos da Warri da Calabar, an samu sauƙi domin ana samun sa a kan ƙasa da naira ɗari huɗu” don haka farashin
zai yi ƙasa a kwanaki masu zuwa a sassa daban-daban na Najeriya.
Danmalam ya danganta faɗuwar farashin man fetur ɗin a kan wasu dalilai biyu da suka haɗar da rashin kuɗi da kuma damuna.
Don haka ana dab da ganin sauyi, saboda ba kowa yake da kuɗin da zai iya siyan mai yanzu ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Masu iya Magana na cewa “abin dariya yaro ya tsinci Hak’ori” wato Maganar da Masa Kance, Mu muke shayarda Makotan K”asashenmu ta tabbata kenan, Ku Lodo shi yayi maku yawa dole kasuwar sa tayi rugu – rugu. wannan Dalilan da kuka fad’a bazasu gamsarda jama’a ba tunda shi bada ruwan sama akeyinsa ba balle ace ruwan saman ne yayi yawa, sabo yazo. Lol