Wani ɗan Najeriya da ya yi aure shekara 12, ya koka kan yadda matarsa ke yi da shi
Alfijir Labarai ta rawaito Sakamakon rashin siyan ragon Sallah, ya ce ta ƙi yi masa magana ko girki ga ‘ya’yansa
Ya faɗa cewar matara bata ƙaunarshi ko goyon bayansa cikin yanayin da ya tsinci kansa a ciki
Ɗan jarida, Lawan Bukar Maigana, ya wallafa a shafinsa na Twitter , ya ce mutumin bai taba sayen rago a duk lokacin bikin Sallah ba tsawon shekaru kusan 12.
Duk da haka, babban bashin da ake binsa da kuɗin makarantar yara ya hana shi siyan ragon a 2023 amma matarsa ba za ta fahimta ba.
Mutumin ya yi kukan cewa lallai zai saya mata karamin rago amma ya lura ba ta ƙaunarsa kasancewar ba ta taba tallafa masa a cikin mawuyacin hali ba.
“Ina da dubu ɗari a aljihuna. Zan je na siyo mata qaramin rago amma Allah ya sani matata ba ta sona domin ba ta tallafa mani kuma ba ta taimaka mini a cikin mawuyacin hali,’’ inji mutumin.
A cewar mutumin, har yanzu bai sake ta ba saboda yaransu.
Dimokuraɗiyya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ