Ganduje Ya Magantu Kan Dakatar Da Albashin Ma’aikata Su Dubu 10 A Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya koka kan dakatar da albashin ma’aikata sama da dubu 10 da gwamnatinsa ta dauka aiki.

Alfijir Labarai ta rawaito tsohon gwamnan ya koka ne ta cikin wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labarai na jihar kano, Muhammad Garba ya fitar a ranar Laraba, na sakon barka da babbar Sallah ga al’ummar jihar Kano .

Ganduje ya ce dakatar da biyan albashin ma’aikatan da ya dauka aiki ya haifar da damuwa a zukatan ma’aikatan kano, a lokacin da jama’a ke fadi tashin yadda zasu tsira da rayuwarsu .

Hakazalika ya kuma nuna damuwarsa kan soke karin girma da kuma na matakin albashi da ya yiwa malaman makarantun firamare, da gwamnatin tayi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ


One Reply to “Ganduje Ya Magantu Kan Dakatar Da Albashin Ma’aikata Su Dubu 10 A Kano”

  1. Amma bai magantu akan dawowa da ma’aikata da yan fansho kudaden dayai wata 38 yana yanke musu ba ko?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *