Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce, wani sojan ruwa na kasar Amurka ya taba gaggaura masa mari lokacin yana direbar taxi a kasar Amurka.
Alfijir Labarai ta rawaito Shugaba Tinubu na cewa da gangan ya caji sojan ruwan kudi masu yawa bayan da ya dauke shi ya kai shi wata unguwa, shi kuma saboda haushin da ya ji sai kawai ya gaura masa mari.
Tinubu ya bayyana hakan ne ta cikin wani kundin tarihinsa rayuwarsa wanda kafafen yada labarai suka wallafa a baya-bayan nan.
Littafin tarihin shugaban kasar mai taken: “Tinubu: My life as gypsy cab driver in the US” fitaccen dan jaridar nan Mike Awoyinfa shine ya rubuta.
Ta cikin littafin tarihin shugaba Tinubu ya ce, yayi aiki a matsayin direban taxi a Chicago, inda yake daukar fasinja daga filin jirgin sama zuwa masaukinsu
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ