Jami’an Tsaro a jamhuriyar Nijar sun damƙe wani Malamin Musulunci mai suna Gausi Almustapha bisa zargin shi da wuce gona da iri, inda ya auri mata saba’in 75 kamar yadda jaridar Taskar Gizago ta rawaito.
Alfijir Labarai ta rawaito Malamin wanda yake zaune a ƙauyen Tudun Faira a yankin Dogon-Dutse na Jihar Dosso, ya yi ƙaurin suna, inda yake ikirarin cewa shi ne Mahadi, wanda zai zo a ƙarshen duniya.
Haka kuma hukumomin na tsaro sun zarge shi da laifin bautar da mabiyansa, inda yake sanya su aikin noma a manyan gonakinsa. Yana kuma aure ‘ya’yansu ba tare da bin tsarin Shari’ar Musulunci ba ta hanyar noman manyan gonakinsa tare da aura masa ƴaƴansu mata.
A halin da ake ciki dai, malamin yana tsare a gidan maza, inda ake shirin yanke masa hukunci.
Labarai24
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Allah yaimana maganinsa
To menene abin mamaki ga mutumin da sunansa Gausi Kuma akace sunan Garinsa Faira sannan Yana ikirarin cewa shine Mahadin karshen zamani don ya auri Mataye 75.
Allah ya tsaremu sa sharrin waddannan shaidanun mutanen
A gaggauta yanke mai hukunchi saboda karwani yai sha awar Aikatawannan.Yana dakyau ma hukunta su Aika da malamai Da gina makarantu A wannan yankunan da Fahimtar dasu Addini. Tare da tallafawa mutanen yankin
Irin wadannan malam ya kamata jama a da hukumomi su dinga Saka Ido akai kafin barnar tayi nisa yanzu mata 75 ai ba karamar illah yayiwa jamaar garin ba domin mata sune tushen rayuwar Al,umma ya kamata ayi gaggawar yanke masa hukunci