Alfijir Labarai ta rawaito Hukumar DDS a Nijeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe wani fitaccen dan bindiga wanda ya taba tserewa daga kurkuku, Kabir Bala wanda aka fi sani da Okwo.
Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce dakarun nata sun kashe Okwo yayin da suka yi ba-ta-kashi da shi da yaransa a jihar Kogi da ke arewacin kasar.
“A wani samamen hadin-gwiwa da safiyar yau, 22 ga watan Yuni, 2023, dakaru sun kai mamaya maboyar Kabir Bala da aka fi sani Okwo, wanda ya taba fasa gidan yari kuma shahararren dan bindiga a Ejule, karamar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
Okwo da ‘yan bindigarsa sun yi ba-ta-kashi da bindigogi da dakarunmu abin da ya kai ga kashe shi, amma sauran sun tsere,” in ji sanarwar
Ta kara da cewa dakarunta sun kuma kwato makamai da suka hada da bindiga uku kirar AK47 wadanda aka makare da harsasai, makamai shida kirar gida da wayoyin salula biyu da kuma layu.
Hakazalika DSS ta kara da cewa wasu rahotanni sun nuna mata cewa wasu na kitsa kai hare-hare yayin bukukuwan sallar layya.
“A nata bangaren, DSS tana kira da a sanya ido sosai gabanin sallar layya, musaman bayan rahotanni sun nuna cewar ana shirin kai hari a wuraren ibada da na shakatawa kafin da kuma yayin bukukuwan sallah,” in ji Afunanya.
Hakan ya fito fili ne sakamakon abubuwan fashewar da aka kama daga hannun ‘yan ta’adda, in ji sanarwar.
Kazalika DSS ta ce dakarunta sun kai samame a jihar Nasarawa kan fitaccen dan bindigar nan Abubakar Muhammad wanda ake kira Abu Direba.
Ta ce yayin samamen, an kwato makamai da alburusai da motoci.
TRT Afrika
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ