An Ga Watan Zhul-Hijjah A Najeriya – Sarkin Musulmi

Alfijir Labarai ta rawaito Mai Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da Litinin, 19 ga watan Yunin 2023, a matsayin 1 ga watan Zhul-Hijjah a Najeriya, sakamakon ganin jinjirin watan a ranar Lahadi.

Hakan dai na nufin ranar Laraba, 28 ga watan Yuni ce za ta kasance ranar Babbar Sallah a Najeriya.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamitin ganin watan ya fitar da yammacin Lahadi,

“Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, yana taya dukkan al’ummar Musulmai barka da Sallah,” in ji Sarkin na Musulmi, wanda kuma shi ne shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA).

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *