Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Yakubu Mahmood ya gabatar da takardu gaban kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa (PEPC) kan karar da Alhaji Abubakar Atiku da jam’iyyar PDP suka shigar.
Kunshin kundin da tuni aka mika shi ranar Alhamis ta hannun mataimakiyar Darakta mai kulada tantance bayanai ta hukumar Misis Morenikeji Tairu, sun hada da Form EC9 na Shugaba Bola Tinubu, wanda shi ne wanda ake kara na biyu a shari’ar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, ya wallafa cewa Form EC9 wata takarda ce da ke nuna goyon bayan bayanan mutanen da ke neman kujerar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa, wanda PDP da Atiku Abubakar ke kalubalantar sahihancin zaben da aka gudanar aranar 25 gawatan fabrairu.
Kotun ta bayar da sammaci ga Mahmood dangane da wasu takardu da suka shafi gudanar da zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu bayan da Atiku ya shigar da kara.
Lauyan wadanda suka shigar da kara, Mista Chris Uche, SAN, ya ce wadanda suka shigar da kara a ranar 26 ga watan Mayu, sun zayyana abubuwa 11 da Mahmood ya gabatar a gaban kotu.
Misis Tairu, ta shaida wa kotun cewa abubuwa hudu ne kawai masu shigar da kara suka nema.
Ta ce abubuwan da ke akwai sune jerin Form EC8D (sakamakon jihohi);
EC8DA (bayani na ƙarshe na sakamako);
Certified True Copy (CTCs) na Rivers Bi-modal Verification Accreditation System (BVAS)

Sauran sun hada da rahoton BVAS daga Jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT) da Form EC9 na Tinubu (bayanan sirri da Tinubu ya kawo wa INEC domin taimakon sa na tsayawa takarar Shugaban kasa).
Lauyan INEC, Mista Abubakar Mahmoud, SAN, da lauya ga Tinubu, Mista Wole Olanipekin, SAN da na jam’iyyar All Progressives Congress, (APC) duk sun nuna adawa da amincewa da takardun a cikin shaida.
Uche, yayin da yake mayar da martani ga matsayin INEC na cewa ba a biya takardun shaida ba, ya nanata cewa ya zuwa yanzu abokan Tinubu ya biya Naira miliyan 6.7 ga hukumar zabe INEC don tantance shi a matsayin Dan takara.
Atiku da PDP na kalubalantar tsarin da sakamakon zaben shugaban kasa ya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairu wanda ya haifar da Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Masu shigar da kara na kuma dagewa kan cewa shugaba Tinubu bai cancanci tsayawa takara ba bisa dalilan da ake zarginsa da yin takara sau biyu da kuma zama dan kasa biyu.
Inda Atiku zaibi Raayina da ya hakura ya taya tinubu gyara Nigeria anma wallahi Atikune na zaba nima
Korai kuwa