Alfijir Labarai ta rawaito an kama Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, tars da gurfanar da shi gaban wata kotun tarayya da ke birnin Miami na Jihar Florida
Ana dai zargin tsohon shugaban ne da wasu jerin tuhumce-tuhumce har guda 37 masu alaka da boye wasu muhimman takardu, zamanin da yake mulki.
Sai dai yayin zaman kotun na ranar Talata, cincirindon magoya bayansa ne suka taru a wajen kotun don nuna goyon bayansu gare shi.
Amma an jibge tarin jami’an tsaro a kewayen kotun, inda aka hana magoya bayan nasa da ma sauran jama’a shiga ciki saboda tsaro.
Trump, wanda ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa neman shugabancin kasar a zaben shekara ta 2024 mai zuwa, ya sha bayyana shari’ar da ake yi masa da bi-ta-da-kulli.

Ana dai sa ran zai yi jawabi ga magoya bayansa da yammacin Talata a Bedminster da ke birnin New Jersey, bayan kammala zaman kotun.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ