Shugaba Tinubu Ya Sake Ganawa Da Kwankwaso A Villa

Alfijr ta rawaito Shugaba Bola Tinubu na ganawa da jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso a fadar shugaban ƙasa, Abuja.

Kwankwaso ne dan takarar shugaban kasa na farko a zaben 2023 mai cike da rudani da ya ziyarci Tinubu a fadar Aso Rock Villa.

A tuna cewa a ranar 16 ga Mayu, Tinubu da Kwankwaso sun gana a Faransa don tattaunawar zaman lafiya.

Rahotanni sun ce shugaba Tinubu ya nemi Kwankwaso da ya tuntubi abokan siyasarsa kan bukatar yin aiki tare.

An ce shugaban kasar da Kwankwaso sun amince da ci gaba da ganawa a gaba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

One Reply to “Shugaba Tinubu Ya Sake Ganawa Da Kwankwaso A Villa”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *