Shugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu Akan Dokar Wutar Lantarki Ta Shekarar 2023

Alfijir ta ruwaito cewa Shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu ya Saka hannu yau Juma’a 09/06/23 akan dokar wutar lantarki ta shekarar 2023.

Ita dai wannan dokar zata maye gurbin wacce akayi a shekarar 2005 ne. Dokar zata jagoranci yadda kamfanoni masu zaman kansu zasu shigo cikin harkar samar da wutar lantarki a Nigeria.

Wasu daga cikin canje canjen da wannan dokar zata kawo sun hada da baiwa jihohin kasar nan damar mallakar kamfanonin samarwa tare da raba wutar lantarki domin ragewa gwamnatin tarayya nauyi.

Haka kuma dokar ta baiwa jihohi damar bada lasisin samar da wutar ga masu zuba jari a jihohin su.

A halin da ake ciki dai tuni Jihohin Kaduna da Edo da Lagos suka samar da dokokin samar da wutar lantarkin a jihohin su. Abunda ya rage musu kawai shine su fara aiwatar da ita.

Sauran jihohin da basu da dokar kuwa sabuwar dokar ta wajabta musu aiki da hukumar daidaita wutar lantarki ta kasa wato (NERC)

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *