Hukumar Alhazai Ta Gindaya Sabbin Sharudda Ga Maniyyatan Nijeriya

Alfijr ta rawaito hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa daga yanzu ba za a yarda wani maniyyaci ya wuce adadin kwanaki biyar a Madina, kafin ya zarce Makka ba.

Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai, Musa Uban Dawaki ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sa wa hannu, ya ƙara da cewa an fito da wannan sabon tsarin ne domin a rage cinkoson masu zuwa ziyara a Madina.

Uban Dawaki ya ƙara da cewa hukumar su ta fara amfani da bin wannan tsari bayan ta tuntuɓi waɗanda ya kamata.

“An fito da wannan tsarin ne bayan da aka yi kuka dangane da ɗimbin yawan ‘yan Najeriya a Madina,”  idan ba a yi gaggawar fito da tsarin ba, to cinkoson ‘yan Najeriya a Madina zai iya fusatar da Gwamnatin Saudiyya har ta ladabtar da ƙasar. In Ji shi.

Ya ce yanzu duk duniya an san cewa tsarin aikin Hajji ya canja, saboda ci gaban zamani.

Aƙalla mutum 96,000 ne za su taki Arfa a bana daga Najeriya.

Tuni dai aka kwashi sama da maniyyata 30,000 daga cikin 96,000 daga Najeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *