
Alfijr ta rawaito wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne sun tare ayarin motocin Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello tare da kai musu hari.
Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya fitar ranar Asabar, ta zargi mutanen da ake kyautata zaton magoya bayan Alhaji Muritala Yakubu Ajaka ne da harin da misalin karfe 12:30 na ranar Asabar.
A cewar kwamishinan, an kai harin ne a kusa da sansanin sojin ruwa da ke da tazarar kilomita kadan daga Lokoja inda ayarin motocin Muritala Yakubu Ajaka da suka ga na Gwamna suka tare hanya, wasu ‘yan barandansa suka fara harbe-harbe a kan ayarin motocin Gwamna.
Wani Tundra mai dauke da tambarin jam’iyyar SDP kuma dauke da tutocin SDP ya toshe motar Gwamna tare da mutanen da ke cikin motar Tundra dauke da gajerun bindigu.
Gwamnan ya bar wurin ba tare da wata matsala ba, kuma babu wani abu da ya sami gwamnan yana cikin kishin lafiya.”
Ko da yake an ce wasu daga cikin hadiman tsaro da wasu na hannun daman gwamnan sun samu raunuka, inda aka garzaya da su asibitoci domin kula da lafiyarsu.
Kwamishinan ya bukaci al’ummar jihar ta Kogi da su kwantar da hankalinsu domin jami’an tsaro na da cikakken iko, domin kamo yan ta’addar da suka kai harin.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta tabbatar da bin doka da oda domin za a hukunta wadanda suka kai harin.
“Gwamnan ya yi gargadin cewa babu wani dan jam’iyyar APC da ya isa ya shiga duk wani harin ramuwar gayya saboda rashin tsaro daga kowane bangare za a fuskanci hukunci mai tsanani,” in ji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇