EFCC Ta Kama Wani Fitaccen Mawaki Da Wasu Tarin Mutane

Alfijr ta rawaito Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta kama wani shahararren mawakin Tiktok, Crown Uzama (wanda aka fi sani da ShalliPopi) da manajansa Ajayi Hafeez (wanda aka fi sani da 21 Badda) da laifin zamba a intanet.

. Kakakin ta, Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ranar Talata a Abuja.

A cewarsa, an kama su ne tare da wasu mutane 29 da ake zargi da su, ciki har da mata hudu: Glory Kelvin-Ogunwa l, Tina Ochonogor, Favor Dawa da Joseph Iya.

“Sauran su ne Adewale Adedokun, Yakubu Ojochememi, AbdulAzeez Suleiman, Umoru AbdulAzeez, Emmanuel Iwebo, Shuaibu Smart, Joel Kator, Gowon Titus, Emmanuel Daniel, Enough Ekpo, Atano Eben, Ijuo Ochi, Paul Kaye, Uyit Victor da David Yachai.

“An kuma kama Leche Sokomba, Onoja Uroko, Cornelius Agbodesi, Edigim Success, Azubuike Oniya, Usman Shereef, Victory Chiemela, Lambert Chikwado, Asoore Oloruntoba da Malik Jibril.

“An kama su ne biyo bayan bayanan sirri da aka samu game da wani shiri da wasu da ake zargin ‘yan damfara ta Intanet suka shirya a Barnawa, Kaduna,” in ji shi.

Ya kara da cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani samame da suka kai a Otal din Disney Park Lounge, Epitome da Tomoso Hotels, duk a yankin Barnawa na Kaduna.

“Abubuwan da aka kwato sun hada da wayoyin hannu, kwamfutocin tafi da gidanka da motoci biyu.

“Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu idan aka kammala bincike,” in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *