Rikici Ya Barke Tsakanin DSS Da EFCC

Alfijr ta rawaito wani rikici tsakanin Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS da jami’an EFCC bayan da jami’an DSS suka hana ’yan EFCC shiga ofishinsu.

Rikicin ya samo asali ne a safiyar Talata, kan mallakar ginin ofishin da hukumomin biyu suke, a kan Titin Awolowo da ke Jihar Legas.

Aminiya ta gano cewa da sanyin safiya ne jami’an DSS suka hana ’yan EFCC da ake aiki a wurin shiga cikin harabar.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce ko da jami’an hukumarsa suka zo aiki da safe, DSS sun hana su shiga harabar.

Wakilanmu ya nemi samun karin bayani daga kakakin DSS, Peter Afunanya, amma bai tabbatar ko kore faruwar hakan ba.

Sai dai ya jaddada cewa hukumarsa ce ke mai mallakar ofishin, kuma hukumomin biyu sun shafe kusan shekaru 20 suna zama tare a harabar.

Ya ce duk da cewa hukumar ce asalin mai wurin, bai kamata a ce ofishin ne EFCC ba ne, ko a ce DSS ta hana ’yan EFCC shiga harabar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *