Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar zamfara, Bello Matawalle ya zargi shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa da neman cin hancin dala miliyan biyu daga gare shi.
Matawalle ya yi wannan zargin ne a wata hira da BBC Hausa a ranar Juma’a, a daidai lokacin da ake ci gaba da takun saka tsakanin gwamnan da hukumar yaki da cin hanci da
rashawa.

Idan za a iya tunawa, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Matawalle ya yi kira ga Bawa ya yi murabus, yana mai cewa yana da tambayoyi da zai amsa kan cin hanci da rashawa.
Sai dai Shugaban na EFCC ya amsa cewa ba shi da wani abin boyewa, yayin da ya bukaci Matawalle da ya kai karar hukumomin da suka dace idan yana da wata shaida a kansa.
Duk da haka, da yake magana yayin hirar, Matawalle ya dage cewa ba za a iya amincewa da Bawa ba.

Ya ce, “Ba wai kawai a rika zargin gwamnoni ba ne. Ba gwamnoni kadai ke da baitulmali ba, gwamnatin tarayya ma tana da ita. Me shugaban EFCC yake yi musu? Kamar yadda yake ikirari yana da hujja akan gwamnoni, bari ya nunawa duniya shedar wadanda ke matakin tarayya.
“Idan ya bar ofis, tabbas mutane za su san shi ba mai gaskiya ba ne. Ina da hujja akansa.
Ya ƙara da cewa abar shi ya bar ofishin, ina gaya muku a cikin dakika 10 watakila sama da mutane 200 za su kawo shaidar cin hancin da ya karba a hannunsu.
Ya san abin da ya nema daga gare ni amma na ƙi.
“Ya nemi cin hancin dala miliyan biyu kuma ina da shaidar hakan.
Ya san gidan da muka hadu, ya gayyace ni ya gaya mani yanayin.
Ya ce min gwamnoni za su je ofishinsa amma ban yi ba.
Idan ba ni da shaida, ba zan faɗi wannan ba. “
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ