Dubun Wasu Da Ake Zargin Ƴan Yahoo Boys Ne Su takwas Ta Cika

Alfijr ta rawaito Hukumar EFCC reshen Abuja, a ranar Laraba, 10 ga Mayu, 2023, ta kama wasu mutane takwas da ake zargi da damfarar yanar gizo.

Wadanda ake zargin sune Usifo Mophy, Eze Richard, Abdulkadir Sadiq da Emmanuel Joseph. Sauran sun hada da Tuoyo Kelvin, Joel Omojevwe, Joshua Omojevwe da Oreva Omojevwe.

An kama su ne a Estate EFAB Estate Gwarimpa da kuma Federal Housing Authority Estate, Nyanya, Abuja, bayan wasu sahihan bayanan sirri game da ayyukansu na damfarar yanar gizo.

Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da wayoyi sama da 10 na kera daban-daban, kwamfyutocin HP, MacBook, motoci Toyota Camry guda 2, mota kirar Mercedes Benz C300 da Lexus RX 350.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *