
Alfijr ta rawaito Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati sun kama tsohon ministan lantarki na Najeriya, Injiniya Saleh Mamman, wata majiya a ma’aikatar lantarki ta tarayya ta shaida wa BBC.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce EFCC ta kama Saleh Mamman ne tun da sanyin safiyar Laraba inda suke ci gaba da tsare da shi a shalkwatar hukumar da ke Abuja.

Sun ce kamen na da alaƙa da zargin almundahanar wasu kuɗaɗe kimanin naira biliyan 22.
A cewarsu, jami’an EFCC sun kama Saleh Mamman ne game da jerin bincike kan zargin aiwatar da wasu ayyukan lantarki.
Rahotanni sun ce ana zargin sa da haɗa baki da wasu jami’ai a ma’aikatar lantarki waɗanda ke kula da asusun ajiyar kuɗaɗen ayyuka a tashoshin lantarki na Mambilla da Zungeru, don karkatar da kuɗi naira biliyan 22, tare da rabawa a tsakanin su.

Kafofin yaɗa labaran sun ce bincike ya bankaɗo wasu kadarori a Najeriya da ƙasashe waje masu alaƙa da jami’an da ake zargi, sannan an ba da rahoton gano miliyoyin nairori da daloli.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ
Tunda yayi fallasar Wutar Mambila Yaya zasu barshi. Ga Fashola daya gayawa Nijeriya cewa an kammala aikin saura budewa alhali ko share inda za’ayi aikin ba’ayiba sabon mukami akeso abashi a gomnatin Tinubu. Sale Mamman Allah yana taredakai