Gwamnatin Najeriya Ta Fara Shirin Sayar Da Asibitin Fadar Shugaban Ƙasa

Alfijr ta rawaito Gwamnatin tarayya, ta fara shirin sayar da Asibitin fadar shugaban ƙasa da wasu sassa da ke ƙarƙashin fadar gwamnatin ta Villa ga ƴan kasuwa.

Babban Sakataren fadar shugaban ƙasa, Tijjani Umar ya ce, ma’aikatar kuɗi da na ma’aikatar ƙasa sun ware wasu ayyuka da tsare-tsare uku a fadar shugaban ƙasa da gwamnati za ta fara yin haɗaka da ƴan kasuwa wajen gudanar da su.

Haka kuma, ya bayyana cewa asibitin fadar shguaban ƙasa da ke Abuja da Lagos na daga ɓangarorin da ake shirin shigo da ƴan kasuwa su zuba jari.

Sauran kadarorin sun haɗa da sashen kula da gandun daji da kuma Dandalin wasan yara na fadar ta shugaban ƙasa.

Tijjani Umar ya sanar da haka ne a jawabinsa ga taron wata uku na farkon shekarar nan da muke ciki kan haɗakar gwamnati da kamfanoni da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa.

A baya yanayin da asibitin na fadar shugaban ƙasa ke ciki ya tayar da ƙura musamman bayan da matar shugaban ƙasa Aisha Buhari ta yi ƙorafi game da rashin magunguna da kayan aiki a asibitin.

Kakaki Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *