
Alfijr ta rawaito Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba a Abuja ya rantsar da sabbin Perm Sec guda shida kafin a fara taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta Tarayya.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa a watan Maris din 2023 ne shugaba Buhari ya amince da nadin Perm Sec.
Shugabar ma’aikata ta tarayya, Dr Folashade Yemi-Esan, a ranar 29 ga Maris, 2023 ta sanar da amincewar shugaban kasa na nadin manyan sakatarorin guda shida da suka yi nasara a zaben da ofishinta ya gudanar.
A lokacin da yake karanta takardar sabbin sakatarorin, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Mista Femi Adesina, ya ce taron ya kasance karshen makonnin da aka kwashe ana gudanar da atisayen tantancewar na daraktoci, wanda ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati ya gudanar.
Wadanda aka rantsar sune:-
Mahmud Kambari (Borno),
Esuabana Nko-Asanye (Cross
River), Adamu Lamuwa (Gombe),
Yakubu Kofar mata (Kano),
Olufemi Oloruntola (Ogun)
Richard Pheelangwah (Taraba).
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ