
Alfijr ta rawaito ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata Kwamishinar Kasa, Hukumar Kidaya ta Kasa a Jihar Bayelsa, Misis Gloria Izonfuo
Daga bisani sun bukaci a ba su Naira miliyan 500 kafin su sako Misis Gloria, wadda suka yi garkuwa da ita tare da ma’aikatanta guda biyu.
An sace Misis Gloria Izonfuo, wadda tsohuwar shugabar ma’aikatan Jihar Bayelsa ce a Jihar Ribas, ranar Lahadi a hanyarta ta zuwa yankin Brass na jihar Bayelsa, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
Maharan sun yi awon gaba da ita ne tare da direbanta da dan aikinta, kamar yadda kakakin ’yan sandan Jihar Ribas, Grace Iringe-Koko ta tabbatar.

kwamishinan ‘yan sanda jihar ya tura runduna ta musamman domin ceto ta da mutanen.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ
Allah ya gyara