Cutar Sanƙarau Ta Hallaka Mutane 118 A Wasu Jihohin Najeriya


Alfijr ta rawaito cutar Sankarau da ta Kunno kai ta kashe mutane 18 a cikin jihohi 22 na Najeriya, daga watan Oktoban Bara zuwa farkon Afrilun da muke ciki.

Bayanai da hukumar kare yaɗuwar cututtuka ta kasa ta fitar a ranar Asabar, ya nuna kananan hukumomin 29 abin ya shafa kawo yanzu.

Jihohin 22 da abin ya shafa sun haɗar da: Kano, Abia, Adamawa, da Bauchi, Bayelsa Benue, Borno, da kuma Ebonyi.

Sauran sune Jihar Gombe, Imo, Jigawa, Katsina, Kebbi, Kogi, Nassarawa, Niger, Oyo, Plateau, Sokoto da kuma Taraba sai Yobe da jihar Zamfara.

Masana sharhin lafiya dai sun ce yanayin zafi da ake fama da shi a yan kwanakin nan a wasu jihohin arewacin kasar nan shi ke kara ta’azzarar yaɗuwar cutar.

Daily Trust

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *