Wasu Jami’an Tsaro Suka Hallaka Mai Jego Da Jaririyarta


Alfijr ta rawaito rundunar ƴan sanda sun tabbatar da cewar jami’an tsaron Civil Defence sun harbe wata mai msta da jaririyarta yar kimanin wata takwas har lahira a Jihar Imo.

Rundunar ta bayyance cewa harsashin da jami’an suka harba ya yi ajalin mai jegon da jaririyarta ne a bisa kuskure, amma ba su ya harba ba kai tsaye.

Wasu majiyoyi a jihar sun ce harsashi ya samu wata mata kuma da ake tunanin mahaifiyar mai jegon ce.

Kakakin rundanar yan sandan jihar ya ce jami’an NSCDC sun yi harbi ne a iska daga kan motar sintirinsu da ke tafiya, amma aka yi rashin sa’a harsashi ya samu matar da ’yarta a lokacin da take jiran motar haya a gefen titi.

Lamarin ya faru ne a ranar Lititin a Mahadar Fire Service da ke garin Owerri, babban birnin jihar.

Okoye ya ce, “Ana gudanar da bincike, amma wani ganau ya shaida mana cewa harsashin jami’an Civil Defence ne ya samu matar da jaririyarta; da aka kai su asibiti kuma likita ya tabbatar da mutuwarsu.”

Amma ya ce duk da bayanin ganau din, za aci gaba da binciken faruwar lamarin.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *