Wasu Manyan Lauyoyin Kano Sun Yi Ƙarar Mawaƙi Dauda Rarara

Alfijr ta rawaito Wasu rukunin lauyoyi a nan Kano sun yi karar Mawakin nan Dauda Kahutu Rarara wajen Maimartaba Sarkin Katsina da Maimartaba Sarkin Daura.

A takardar da suka aike wa Sarakunan sun bayyana kokensu kan zargin Rarara da yin wakoki yana aibata manyan yan siyasar jihar Kano.
Sannan wakokin suna janyo zage-zage da cin zarafi a tsakanin jama’a.
Lauyoyin sun kuma ba wa Rarara shawarar ya gyara harshensa a gaba, sannan ya fito ya nemi afuwa ko kuma su dauki mataki na gaba.

Barr. Badamasi Sulaiman Ganduje shi ne jagoran wadannan lauyoyi ya yi karin bayani a kai.

A cikin wakokinsa ya taba wasu manyan jihar masu kololuwar daraja da muhubba a jihar kamar Malam Ibrahim Shekarau
Engr Rabiu Kwankwaso
Sarki Muhammadu Sanusi ll

Ya kira malam Ibrahim Shekarau da kiransa da Duna!

Hakazalika ya kira Engr Rabiu Musa da Tsula.

Bai tsara nan ba ya sake kiran sarki mai daraja na Kano da sunan dabba wato Carki!

Wannan salo a gaskiyance salo ne da ya sabawa dokokin kasa, domin sukan kawo tarzoma wanda doka bata aminta ba kuma sun yi karo da koyarwar Islama, da al adunmu.

Duba da talakan su ne yasa muka aikewa sarkin Daura da masarautar Katsina duba da sana arsa mai kyau ce a tsaftace masa ita ba don a hana shi ba.

Idan aka kalla za a ga Rarara yayi waka ya yafi jihar Katsina da cewar Jahata jahata ce, bai taba zagin taba! To don me zai zo ya na zagar mana tamu jihar? Bayan jihar ce ta masa riga da wando.

A karshe muke kira da Mawaƙin da ya fito ya tuba kuma ya sauya salon wakarsa domin a zauna lafiya.

Freedom Radio

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

2 Replies to “Wasu Manyan Lauyoyin Kano Sun Yi Ƙarar Mawaƙi Dauda Rarara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *