Wata Mata Ta Maka Mijinta Gaban Kuliya Kan Kin Kaita Kasar Saudiyya

Alfijr ta rawaito wata Mata Mai Suna Karima Nuhu Mai Shekaru 45 Ta maka mijinta Musa Falalu a gaban wata kotun shari’a da ke zamanta a Rigasa a Kaduna bisa zargin kin kai ta Saudiyya.

Mai shigar da karar da ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ta shaida wa kotun cewa ta yi aure da Falalu tsawon shekara hudu inda ya ba ta abinci tsawon wata biyu kacal.

“Ya shaida min cewa ya rasa aikinsa na direba amma ya samu wani a Saudiyya, inda ya bukace ni da in yi hakuri yayin da ya yi alkawarin kaini can.

“Ya zuwa yanzu, ina ciyar da kaina. Har ma na ba shi rancen kudi domin ya samu kudin tafiyar, amma bayan samun abin da yake so sai ya sake ni,” inji ta.

Matar ta shaida wa kotun cewa ba ta da wani shaida sai Allah da zai hukunta su a ranar karshe.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta zargin yana mai cewa ba gaskiya bane.

Ya shaida wa kotu cewa ya sake ta tuni.

Alkalin kotun, Malam Anas Khalifa, wanda ya tabbatar da rabuwar aure tsakanin ma’auratan, ya ce kotun za ta saurari karar mai karar ne kawai idan ta na da shaidu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *