
📸 NSCDC Facebook
Alfijr ta rawaito Hukumar Tsaro da Civil Defence (NSCDC) reshen jihar Kano, ta ce ta kama mutane akalla 93 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar tsakanin watan Janairu zuwa Maris.
Mista Adamu Salihu, Kwamandan NSCDC na jihar ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Kano ranar Juma’a.
Salihu ya ce an kama wadanda ake zargin ne da laifin sata, barna da cin amana da sauransu.
“Daga cikin wadanda ake tuhuma 93, 29 an gurfanar da su a gaban kotu, 57 da ake tuhuma suna kan bincike kuma mun samu hukunci guda bakwai a cikin wannan lokaci,” inji shi.
Kwamandan ya nanata kudurin NSCDC na karewa da kuma kiyaye duk wasu muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa.
Ya bukaci mazauna yankin da su tallafa wa jami’an tsaro da bayanan tsaro masu amfani don kiyaye zaman lafiyar jihar, ya kara da cewa tsaro ya zama alhakin kowane dan kasa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ